25 Nuwamba 2020 - 18:02
​Bayan Saudiyya, Netanyahu Zai Kai Ziyara A Bahrain Da UAE A Mako Mai Zuwa

Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahoton cewa, firayi ministan gwamnatin yahudawan Isra’ila Benjamin Netanyahu na shirin kai ziyara a kasashen Bahrain da UAE a mako mai zuwa.

Shafin yada labarai na Isra’ila i24 ya bayar da rahoton cewa, a cikin mako mai zuwa, Netanyahu zai kai ziyara a kasashen Bahrain da kuma UAE a cikin mako mai kamawa.

Shi ma a nasa bangaren firayi ministan gwamnatin yahudawan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya wallafa wani bayani a jiya a shafinsa na twitter cewa, zai kai ziyara a kasar Bahrain nan bad a jimawa ba, bayan da sarkin kasar ta Bahrain Salman Bin Hamad Al Khalifa ya aike masa da goron gayyata a hukumance.

Netanyahu ya ce ya yi magana da mahukuntan Bahrain ta wayar tarho, kuma nan ba da jimawa ba zai ziyarci kasar, domin ganawa da sarki Salman Bin Hamad da sauran jami’ai.

Ministan harkokin wajen kasar Bahrain ya bayyana cewa, a ziyarar da ya kai Isra’ila a makon da ya gabata, ya mika wa Netanyahu sakon goron gayyata daga sarkin kasar ta Bahrain.

Bisa rahotanni da kafofin yada labaran Isra’ila suka bayar, a daren Lahadi kashe garin Litinin da ta gabata ce Benjamin Netanyahu ya yi wata tafiya ta sirri zuwa Saudiyya Saudiyya, inda ya gana da yarima mai jiran gadon kasar ta Saudiyya Muhammad Bin Salman, sai dai ministan harkokin wajen kasar ta Saudiyya ya karyata rahoton, amma Benjamin Netanyahu da gwamnatin Isra’ila ba su karyata hakan ba, amma sun bayyana rashin jin dadi kan yadda labarin ya bayyana.

342/